IQNA

A Karon Farko Wata Mace Sanye Da Lullubi Na Gabatar Da Shirin Talabijin A Jihar Connecticut A Amurka

22:57 - December 29, 2021
Lambar Labari: 3486756
Tehran (IQNA) Wata mata sanye lullubi ta zama ta farko da ke gabatar da shirin talabijin a bangaren labarai a jihar Connecticut ta Amurka

<p "="" style="box-sizing: border-box; margin: 0px 0px 15px; font-size: 14px; line-height: 1.6em; border: none; background: none; box-shadow: none; color: rgb(51, 51, 51); font-family: Arial, Helvetica, Verdana, Tahoma, sans-serif; font-style: normal; font-variant-ligatures: normal; font-variant-caps: normal; font-weight: 400; letter-spacing: normal; orphans: 2; text-align: start; text-indent: 0px; text-transform: none; white-space: normal; widows: 2; word-spacing: 0px; -webkit-text-stroke-width: 0px; text-decoration-thickness: initial; text-decoration-style: initial; text-decoration-color: initial;">Shafin Kuwait News ya bayar da rahoton cewa, Wata mata ‘yar asalin kasar Masar da ke sanye lullubi ta zama mace ta farko mai gabatar da shirin talabijin sanye da lullubi a bangaren labarai a jihar Connecticut ta Amurka.

"Ayah Jalal" 'yar jarida ce Ba'amurkiya wacce aka zaba a matsayin mai gabatar da shirye-shiryen labaran talabijin ta farko da da ked a lullubi a kanta a jihar Connecticut ta Amurka.

Ayah Jalal ta sanar da wannan zabin a cikin wani sakon da ta wallafa a shafinta na twitter kuma ta rubuta cewa tana jin dadin wannan aiki nata, kuma hakan nasara ce gare ta da ma musulmi.

Shafin CT Insider ya nakalto Ayah tana mai cewa tana tsoron kada hijabinta ya hana a karbe ta a matsayin ‘yar jarida a TV da hana ta fitowa a gaban na’urar daukar hoto.

Ayah Jalal ta rubuta a tarihin rayuwarta cewa mahaifanta ‘yan asalin kasar Masar ne, amma ita an haife ta kuma ta tashi a birnin Connecticut na Amurka; taa kammala karatunta na digiri a aikin jarida da kimiyyar siyasa sannan ta yi aiki a matsayin mai ba da rahoto a jami'a.

Kafin kammala karatunta, ta lashe lambar yabo ta Jami'ar Connecticut Achievement Award.

Ayah Jalal ta shiga tawagar labarai ta WFSB shekaru 3 da suka gabata.

4024499

Abubuwan Da Ya Shafa: lullubi kasar masar hijabi aikin jarida amurka
captcha