IQNA

An Kori Wata Mata Daga Aiki A Ingila Saboda Cire Wa Wata Musulma Lullubi Da Ke A Kanta

23:21 - December 31, 2021
Lambar Labari: 3486763
Tehran (IQNA) An kori wata ma'aikaciya a wani shahararren shago a Ingila saboda cire gyale na abokiyar aikinta musulma.

Shafin Al-arabi ya bayar da rahoton cewa, An kori wata ma’aikaciya 'yar kasar Birtaniya a wani shahararren kantin sayar da kayan abinci bayan da ta cire wa abokiyar aikinta musulma lullubi a lokta biyu daban-daban.

Jaridar Daily Mirror ta rawaito cewa Natalie McGonigel ta gaza tabbatar da cewa korar da aka yi mata, ba a yi hakan kan ka'ida ba, bayan da ta yi ikirarin cewa ta aikata hakan ne a matsayin wasa da raha, inda kotu ta yanke hukunci kan ma'aikaciyar kantin da cewa ta ci zarafin musulmar ne.
 
Kotun da’ar ma’aikata ta Biritaniya ta ce cire mayafin da McGonigel ta yi ya nuna rashin mutunta addinin abokiyar aikinta ne.
 
An kori McGonigel kwanaki shida bayan abokin aikiyarta ta shigar da kara a kanta, kuma an fara binciken ladabtarwa a kanta.
 
Kotun ta saurari kalaman wasu ma’aikatan da lamarin ya faru a gaban idanunsu, sun kuma tabbatar da cewa abokiyar aikinsu 'yar kasar Birtaniya ta cire hijabin abokiyar aikinta har sau biyu.
 
https://iqna.ir/fa/news/4024813
Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha