IQNA

Hamas Ta Gargadi Isra'ila Kan Ci Gaba Da Kai Hare-Hare A Zirin Gaza

19:54 - January 02, 2022
Lambar Labari: 3486770
Tehran (IQNA) kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta gargadi Isra'ila kan ci gaba da kai hare-hare a kan yankunan zirin Gaza.

Shafin Dunyal watan ya bayar da rahoton cewa, kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta gargadi Isra'ila kan ci gaba da kai hare-hare a kan yankunan zirin Gaza.
 
Kakakin kungiyar ta Hamas Hazim Kasim ne ya sanar da hakan a yau , inda ya jaddada cewa hare-haren Isra'ila ba za su wuce ba tare da martani ba.
 
A safiyar yau Lahadi ne jiragen yakin yahudawan sahyoniya suka kai hari a sansanin horas da dakaun Al-Qassam Brigades na Qadisiyah a yankin Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza.
 
Jiragen yaki da jirage masu saukar ungulu na yahudawan sahyuniya sun kaddamar da hare-hare har sau takwas a yankin na Qadisiyah, inda suka yi barna a wuraren da suka kai harin, amma ba a samu rahoton asarar rayuka ba.
 
A birnin Beit Lahia da ke arewacin zirin Gaza, kusa da kan iyaka da yankunan da aka mamaye, jiragen yakin yahudawan sun yi ruwan bama-bamai a kusa da wasu shingaye da suka raba yankin zirin gaza dad a sauran yankunan Falastinawa da Isra’ila ta mamaye.
 
Har ila yau jiragen yakin na Isra’ila sun harba wasu makaman a kan yankunan da ke gabashin garin Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gaza.
 
Tashar talabijin ta Al-Aqsa mai alaka da kungiyar Hamas ta bayar da rahoton cewa, dakarun kungiyar ta Hamas sun kai hari da makaman kakkabo jiragen yaki a kan daya daga cikin jiragen yakin na Isra’ila , inda suka yi amfani da makami mai linzami.
 

4025297

 

 

 

 
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha