IQNA

Koriya Ta Kudu Za Ta Bunkasa Harkokin Yawon Bude Ido Ga Musulmi A Kasarta

19:58 - January 03, 2022
Lambar Labari: 3486774
Tehran (IQNA) Gwamnatin kasar Korea ta kudu na kokarin bunkasa harkokin yawon bude ido ga musulmi a cikin kasarta.

A kokarin da gwamnatin kasar Korea ta kudu take na bunkasa harkokin yawon budea kasar, ta zimmar ganin ta kara kyautata bangarorin da za su jawo hankulan msuulmi zuwa kasar.
 
Daga cikin abubuwa da ma’aikatar kula da harkokin yawon bude ta kasar Korea ta kudu take mayar da hankali a kansua halin yanzu, har da samar da wurare na abincin halal, wanda shi ne abu mafi muhimmanci ga musulmi a lokacin da suke yin tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya.
 
Baya ga haka kuma da samar da wurare da musulmi za su iya gudanar da harkokinsu na addini kamar masallatai a wurare na musamman, da kuam samar da littafai a dakunan karatu na nazarin addinin muslunci.
 
Tun daga shekara ta 2016 dai kasar Korea ta kudu ta yi la’akari da cewa, kudin shigar da take samu daga bangaren yawon bude ido, fiye da kashi 5.3 daga musulmi masu zuwa yawon bude ido a kasar, duk kuwa da karancin abubuwan da suke bukata na halal, wanda kuma samar da wadatattun abubuwa na halal a kasar zai kara yawo hankalin msuulmi matuka zuwa kasar.
 
 

4018803

 

 

 

 
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha