IQNA

Pakistan Ta Yi Allahwadai Da Cin Mutuncin Matan Musulmi A Indiya

18:25 - January 06, 2022
Lambar Labari: 3486786
Tehran (IQNA) Ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta yi Allah wadai da cin zarafin mata musulmi da ake yi a kasar Indiya, inda wasu masu kyamar musulmi suke sanya fitattun mata musulmi na a matsayin gwanjo na sayarwa ta hanyar yanar gizo.

Ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana matakin a matsayin "abin takaici" da nufin wulakanta mata musulmi a Indiya da ma na duniya baki daya.

A cikin sanarwar, Pakistan ta sake yin kira ga kasashen duniya musamman Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa da su dauki matakin dakile kyamar Musulunci da munanan hare-haren da ake kai wa musulmi a Indiya.

A baya-bayan nan ne aka saka hotunan wasu fitattun mata musulmi ‘yankasar Indiya sama da 100 da suka hada da ‘yan jarida da masu fafutuka da kuma ‘yan wasan kwaikwayo a wani shafin yanar gizo ba tare da izininsu ba, sannan aka bayyaa a matsayin hajar sayarwa.

Jami'an Indiya sun ce sun fara guanar da bincike kan lamarin, ‘yan sandan New Delhi sun bude binciken ne bayan samun korafi daga EsmatAra, wata ‘yar jarida wadda kuma aka sanya sunanta a wani shafin yanargizo mai suna Bulli Bai.

An dora daruruwan hotunan mata musulmi a shafin GateHub, kuma an bukaci masu amfani da su shiga domin duba abin da aka kira da "gwanjo” wato hotunan matan musulmi.

Wannan lamari dai ya harzuka da dama daga cikin musulmin kasar ta India, da ma wasu daga cikin wadanda ba musulmi ba, wadanda suke nuna damuwa kan abin da musulmin suke fuskanta.

 

https://iqna.ir/fa/news/4026601

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha