IQNA

Addu'a Ta Bai Daya Tsakanin Musulmi Da Kirista A Kamaru Domin Samun Zaman Lafiya

22:43 - January 08, 2022
Lambar Labari: 3486794
Tehran (IQNA) Daruruwan Musulmi da Kirista ne suka yi addu’ar samun zaman lafiya a Yaounde babban birnin kasar Kamaru, gabanin gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Jaridar Cameroon Tribune ta bayar da rahoton cewa, Sama da limaman Musulmi da Kirista 60 ne suka halarci taron addu’ar, ciki har da Jean Ambarga, Archbishop na Yaounde, da Sheikh  Suleiman Buba, daya daga cikin shugabannin Musulman birnin.

A cikin addu’ar tasa wadda aka karanta cikin harshen Larabci, Buba ya roki Allah da ya kare ’yan wasan kwallon kafa da magoya bayansu da jami’an wasa da ke zuwa kasar Kamaru domin hslsrtsr gasar cin kofin nahiyar Afirka.

A ranar gobe Lahadi (9 ga Janairu) ne ake fara gasar kwallon kafa ta Afirka, kuma za a gudanar da gasar a sassa daban-daban na kasar ciki har da kasashen Yamma, Inda 'yan aware masu magana da Ingilishi suka yi alkawarin kawo cikas ga wasannin.

'Yan sanda sun ce mahara sun tayar da bam a daya daga cikin garuruwan da za su dauki nauyin wannan gasa a ranar Alhamis da ta gabata, amma babu wanda ya jikkata.

Embarga ya ce ya san 'yan Kamaru na son kwallon kafa sosai, kuma ya kamata gasar cin kofin Afrika ta zama sabon mafari na zaman lafiya, da karfi da hadin kan Kamaru, Musulmi da Kirista sun yi addu’a tare da fatan Allah ya baiwa ‘yan wasa da jami’an gasar da kuma masu sha’awar kwallon kafa da za su halarci gasar a Kamaru nasara da kuma zaman lafiya ga kasar da al'ummarta.

 

4026960

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: garuruwa ، magana ، kasar Kamaru ، magoya bayansa ، Musulmi da Kirista
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha