IQNA

Turkiyya na raba kwafin kur'ani 50,000 a Falasdinu

21:37 - January 10, 2022
Lambar Labari: 3486803
Tehran (IQNA) A wani bangare na sabon shirinta na isar da kwafin kur'ani mai tsarki 50,000 ga masallatai da cibiyoyin koyar da kur'ani na Palasdinawa, Cibiyar da ke kula da harkokin addini ta Turkiyya ta kai kwafin 20,000 a zirin Gaza.

Kungiyar Dastak ta kasar Turkiyya dake gudanar da ayyukanta a zirin Gaza ta gabatar da mujalladi 20,000 na kur'ani mai tsarki ga ma'aikatar wakafi da harkokin addini a Gaza a ranar Lahadin da ta gabata don rabawa a masallatai da cibiyoyin koyar da haddar kur'ani.

Hani Suray, shugaban kungiyar Ghazi Dastak, ya ce rabon wadannan kwafin wani bangare ne na isar da sakon "Al-Qur'ani,  wanda aka gudanar a karkashin kulawar wata cibiyar kula da harkokin addini ta Turkiyya.

Ya kara da cewa: Kimanin mujalladi 50,000 na kur'ani ne za a raba a kasar Falasdinu a wani bangare na wannan aiki, inda za a raba mujalladi 20,000 ga Gaza da mujalladi 30,000 ga yammacin gabar kogin Jordan, ciki har da birnin Kudus.

Surayya ya jaddada cewa, za a raba kwafin kur'ani mai tsarki da aka kaiwa ma'aikatar kula da addini ta Gaza a masallatai da da'irorin haddar kur'ani.

4027547

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha