IQNA

An rusa Majalisar Musulmin Faransa

22:35 - January 11, 2022
Lambar Labari: 3486807
Tehran (IQNA) Gwamnatin kasar Faransa ta maye gurbin majalisar musulmin kasar Faransa da wata cibiya mai suna majalisar musulunci a kasar Faransa.

Tashar France 24 ta bayar da rahoton cewa, daukar wannan matakin na zuwa ne domin aiwatar da wani daftarin kudiri mai suna Charter of Islamic Principles a kasar Faransa, wanda wasu kungiyoyin addinin musulunci a kasar suke ganin barazana ce ga hakki da hadin kan  musulmi.

Gwamnatin Faransa ta sanar da kafa wata cibiya mai suna "Majalisar Musulunci a Faransa" domin maye gurbin majalisar musulmin Faransa, wadda a cewar gwamnatin bayan shekaru 20 da kafuwarta ke fama da rikice-rikice na cikin gida.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ya amince da shirin, kuma nan ba da jimawa ba za a gudanar da wani taro mai suna Majalisar Musulunci tare da wakilan musulmi a kasar.

Shi ma shugaban majalisar musulmin kasar Faransa Mohammad Mousavi ya bayyana goyon bayansa ga kafa majalisar musulunci, yana mai cewa majalisar ba ta iya ci gaba da gudanar da ayyukanta, don haka ya kamata a rusa ta; Sai dai kawo yanzu ba a bayyana adadin kungiyoyin Musulunci nawa suke son shiga sabuwar cibiyar ba.

A watan Nuwamban da ya gabata ne gwamnatin Faransa ta sanar da kafa Majalisar limamai ta kasa (CNI) a kasar Faransa a wani bangare na yaki da abin da ta kira Musulunci mai tsatsauran ra'ayi, wanda wasu ke ganin ya gurgunta ayyukan Musulunci a Faransa.

Kasar Faransa dai na da musulmi kusan miliyan shida, kuma kyamar Musulunci ta kara tsananta a shekarun baya-bayan nan, da sunan yaki da tsatsauran ra'ayi.

 

4027814

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha