IQNA

Bayanin Hizbullah Dangane Da Yanayin Da Ake Ciki A Lebanon

18:53 - January 16, 2022
Lambar Labari: 3486827
Tehran (IQNA) Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da kungiyar Amal sun fitar da wata sanarwa inda suka bayyana matsayarsu kan komawa halartar taron majalisar ministocin kasar bisa bukatar al'ummar kasar.

Shafin al-ahad ya bayar da rahoton cewa, Sanarwar ta ci gaba da cewa, a yau kasar Lebanon tana fuskantar matsalar tattalin arziki da tabarbarewar kudi da ba a taba ganin irinta ba, babban abin da ke nuna hakan shi ne tabarbarewar darajar kudin kasar da kuma raguwar ayyukan yau da kullum musamman a bangaren wutar lantarki da kiwon lafiya.

Kungiyar Hizbullah da kungiyar Amal sun jaddada a cikin sanarwar cewa: Mafitar wadannan rikice-rikicen ita ce samar da gwamnati mai karfi da za ta iya samun amincewar kowa da kowa, kuma mun ba da hadin kai ga sauran kungiyoyi tare da bayar da dama wajen kafa gwamnati mai ci a yanzu.

Da suke sukar ayyukan da ba sa bisa ka'ida, na mai binciken harin bam a tashar jiragen ruwa na Beirut da kuma keta doka da sanya siyasa a cikin aikinsa, manyan kungiyoyin biyu sun ce: "Lura da wadannan ayyuka da suka saba wa doka, mun kai ga yanke shawarar dakatar da shiga cikin zaman majalisar ministocin, da nufin tilastawa bangaren zartarwa kula da wannan batu.

Hizbullah da kungiyar Amal sun bayyana cewa: Za mu ci gaba da kokarin gyara tsarin shari'a a cikin wannan harka da kuma kaucewa siyasa da yin aiki domin tabbatar da adalci, don haka dole ne bangaren zartarwa ya dauki matakin kawar da duk wani cikas da ke hana ruwa gudu a kwamitin bincike na majalisa.

 

4028835

 

 

 

captcha