IQNA

Tsohon Shugaban Jam'iyyar Labour Ta Burtaniya Ya Caccaki Gwamnatin Bahrain Kan Murkushe 'Yan Adawa

18:58 - January 16, 2022
Lambar Labari: 3486828
Tehran (IQNA) Tsohon shugaban jam'iyyar Labour ta Burtaniya ya yi kira da dauki mataki kan gwamnatin Bahrain kan murkushe 'yan adawar siyasa da take yi.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, Tsohon shugaban jam'iyyar Labour ta Burtaniya, yayin da yake bayyana goyon bayansa ga masu fafutuka da aka daure a Bahrain, ya yi kira ga kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Johnson da kada ta nuna halin ko-in-kula kan take hakkin bil'adama da ake yi a Bahrain.

Jeremy Corbyn, tsohon shugaban jam'iyyar Labour ta Burtaniya, ya bi sahun gungun 'yan siyasa a Biritaniya da suka yi kira ga gwamnatin Boris Johnson da ta tashi tsaye kan cin zarafin da ake yi a Bahrain tare da neman a sako fursunonin siyasa da aka garkame su a gidajen kaso na masarautar kasar.

Corbyn ya bayyana a shafinsa na twitter cewa, "Yau ne Dr. Abdul Jalil al-Sankis ke cika shekaru 60 a duniya, wanda ke tsare a gidan kason Bahrain saboda dalilai na siyasa, wanda kuma ya shafe kwanaki sama da 190 yana yajin cin abinci.

Dan siyasar na Biritaniya, wanda ya shahara da matsayinsa na nuan goyon baya fursunonin siyasa da wadanda ake zalunta a ko’ina a duniya, ya jaddada bukatar yin kira ga gwamnatin Boris Johnson da ta saki fursunonin siyasa a Bahrain, yana mai cewa kamata ya yi Birtaniya ta sanya baki domin sakin Dr. Abdul jalil.

Jeremy Corbyn ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, "Mun zo nan ne domin yin magana kan adalci da kare hakkin bil'adama a duniya, kuma a yau hankalinmu yana kan Bahrain, ina fata za su ji."

 

4028888

 

 

 

captcha