IQNA

22:21 - January 24, 2022
Lambar Labari: 3486862
Tehran (IQNA) Ofishin jakadancin Amurka ya shawarci ‘yan kasar da ke UAE da su dauki gargadin tsaro da muhimmanci biyo bayan wani farmakin ramuwar gayya da dakarun yemen suka kai a kasar.

Ofishin jakadancin Amurka a Hadaddiyar Daular Larabawa ya yi kira ga daukacin al'ummar kasar da su kiyaye matakan tsaro sosai domin kada su jefa rayuwarsu a cikin hadari.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da sojojin Yemen da kuma dakarun sa kai na kabilun larabawan kasar suka kai hare-haren mayar da marani kan  Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya a safiyar yau, sakamakon hare-haren da suke kaddamarwa kan al’ummar kasar Yemen.

 Sojojin Yaman sun kai hari kan wurare masu muhimmanci a Dubai da Base Air Base na Al-Zafra da  makamai masu linzami a Abu Dhabi a ranar Litinin, 24 ga Fabrairu.

Mohammed al-Bakhiti, mamba a majalisar siyasar Ansarullah ta Yemen a wata hira da tashar Amayadeen ya bayyana cewa, " Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi watsi da shawarar da muka ba ta game da yakin Yemen, kuma a yanzu muna bayar da shawara ga masu zuba jari a UAE da su fice daga kasar.

4031048

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: