IQNA

Sojojin Isra'ila sun kai wa Falasdinawa hari a gabashin birnin Kudus

20:07 - January 28, 2022
Lambar Labari: 3486878
Tehran (IQNA) Sojojin yahudawan sahyoniya sun kai hari a gabashin birnin Kudus a kan wasu gungun matasa Falasdinawa da suke wasa cikin dusar kankara tare da jikkata wasu da dama daga cikinsu.

'Yan sandan gwamnatin mamaya a birnin Kudus sun fatattaki tare da far wa matasan Falastinawa da suka fita wasa da dusar kankara a kofar garin Al-Issawiyah dake arewa maso gabashin birnin Kudus da yammacin jiya.

Yahudawan sahyuniya sun harba harsasai da bama-bamai masu sauti kan Falasdinawa, lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatar wasu da dama daga cikin matasan.

‘Yan mamaya sun kuma kama wasu matasa biyu, tare da rufe hanyar shiga birnin tare da hana ‘yan kasar shiga da fita.

A jiya ne sojojin mamaya suka raunata wani matashi da harsashin bindiga a kofar shiga birnin sannan suka kama shi.

A garin Jabal al-Mukbar da ke kudu maso gabashin birnin Kudus da aka mamaye, sojojin mamaya sun kame wani matashin Bafalasdine a lokacin da ya ke wasa a garin dusar kankara.

Sojojin mamaya sun kuma kama wasu samari 24 daga garuruwan Kudus a daren jiya da safiyar yau, yawancinsu daga garin Al-Tour.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4031854

captcha