IQNA

Cibiyoyin Al-Qur'ani a Sudan sun koma bakin aiki

22:35 - January 30, 2022
Lambar Labari: 3486885
Tehran (IQNA) Gwamnatin kasar Sudan ta sanar da cewa, za a ci gaba da gudanar da ayyukan kur'ani mai tsarki da kuma ilimin addinin muslunci na kasar  da kuma la'akari da mawuyacin halin da ake ciki na siyasa.

Ministan kula da harkokin addini na kasar Sudan Abdul Ati Ahmad Abbas ya bayar da umarnin ci gaba da gudanar da ayyukan kur'ani mai tsarki da kuma sauran harkoki na al'ummar musulmi a babban birnin kasar da larduna.

Kwamitin rusa gwamnatin Omar al-Bashir a Sudan ya sanar shekara guda kafin rusa kungiyoyi da dama, yana mai nuni da dokar rusa gwamnatin kasar da ta hau mulki a ranar 30 ga watan Yunin 1989 da kuma dokar dawo da kadarorin gwamnati da aka kafa a shekarar 2019, wadda ta hada da al'ummar kur'ani mai tsarki na kasar Sudan.

Halin da ake ciki a Sudan ana cikin rudani a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar  a titunan kasar da kuma kiraye-kirayen nuna rashin amincewar al'ummar kasar da mulkin sojoji.

Al'ummar Sudan dai na bukatar a dawo da doka da oda da kawo karshen mulkin soja; Musamman tun bayan ganawar sirri da tafiye-tafiye tsakanin sojojin Sudan da jami'an gwamnatin sahyoniyawan a cikin shekarar da ta gabata lamarin da ya harzuka 'yan Sudan.

Kasar Sudan mai yawan al'umma miliyan 43 da albarkatun kasa da ma'adinai, a ko da yaushe tana fama da matsalolin tattalin arziki, kuma yarjejeniyar sulhu da gwamnatin yahudawan Isra'ila ba ta taimaka wajen rage matsalar tattalin arzikin kasar ba.

4032324

 

 

captcha