IQNA

Hukumar kula da harkokin addini a Turkiyya ta sanar da lokacin ganin watan Ramadan

23:18 - January 30, 2022
Lambar Labari: 3486887
Hukumar kula da addinin kasar Turkiyya ta sanar da ganin ranar farko ta watan Ramadan a shekara ta 1443 bayan hijira.

Hukumar ta sanar a jiya Asabar 29 ga watan janairu cewa watan Ramadan na 1443 zai fara ne a ranar 2 ga Afrilu, 2022. 

Hukumar kula da harkokin addinin Turkiyya ta kuma jaddada cewa, Idin karamar Sallah zai kasance  a ranar 1 ga Mayun 2022.

A halin da ake ciki, masana ilmin taurari sun sanar da cewa ganin jinjirin watan Ramadan a kasashen Larabawa zai kasance ne 2 ga Afrilu, 2022.

Ana kuma hasashen cewa watan Ramadan mai zuwa zai cika kwanaki 30 kuma zai kare a yammacin Lahadi 1 ga Mayu, 2022 .

Kwamitin Shari’ar Musulunci da ke da alaka da Darul Ifta na kasar Masar shi ma ya sanar da cewa a ranar 1 ga Afrilu, 2022, kwamitin zai gudanar da shirye-shiryen dubar watan Ramadan, amma ana hasashen cewa ranar 2 ga watan Afrilu za ta zama farkon watan Ramadana kasar Masar.

Dangane da ranar da za a gudanar da Sallar Idi, kwamitin ya kuma bayyana cewa, domin ganin jinjirin watan Shawwal, kwamitin zai fara dubar watan Shawwal a ranar 29 ga watan ramadan. 

4032390

 

 

 

 

captcha