IQNA

Hamas Ta Yi Allawadai Da Ziyarar Shugaban Isra'ila A Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE

22:27 - January 31, 2022
Lambar Labari: 3486888
Tehran (IQNA) Hamas ta caccaki kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) kan barin shugaban kasar Isra'ila Isaac Herzog ya ziyarci kasar

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta caccaki kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) kan barin shugaban kasar Isra'ila Isaac Herzog ya ziyarci kasar Larabawa a daidai lokacin da a cewarta Isra’ila ke ci gaba da aikata laifuka da kuma mamayar Falasdinu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta yi Allah-wadai da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa kan irin wannan ziyara, tana mai jaddada kakkausar suka da yin watsi da duk wani nau'i na dangantaka da gwamnatin mamaya ta Isra’ila da shugabanninta.

Hamas ta ce wannan ziyarar ta faru ne a daidai lokacin da gwamnatin Isra'ila take ci gaba da take hakkokin al'ummar Falasdinu a yankin Gabashin Quds da ta mamaye da yammacin kogin Jordan da kuma yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya.

Kungiyar gwagwarmayar ta Falasdinun ta kuma yi gargadin cewa tarbar shugabannin Isra'ila a kasashen Larabawa zai karawa Isra'ila kwarin gwiwar kara aikata laifuka kan Falasdinawa.

 

4032519

 

 

captcha