IQNA

Baje Kolin Sana'o'in Hannu na Kasar Iran Karo na 35

Tehran (IQNA) - An bude bikin baje kolin kayayyakin hannu na kasa karo na 35 na kasar Iran a ranar 29 ga watan Janairu a filin baje kolin kasa da kasa na dindindin na Tehran.

An BUDE baje kolin sana'o'in hannu da masu fasaha 211 daga sassa daban-daban na Iran suka yi, kuma taron zai ci gaba da gudana har zuwa ranar 2 ga watan Fabrairu.