IQNA

19:02 - February 06, 2022
Lambar Labari: 3486915
Tehran (IQNA) Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga hukumar kare hakkin bil adama ta MDD da ta ziyarci lardin Xinjiang na kasar Sin dmoin sanin halin da musulmi suke ciki.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin kasar Sin da su ba da damar ziyartar halin da ake ciki a yankunan 'yan kabilar Uyghur.

A cewar MDD, Antonio Guterres ya shaidawa shugabannin kasar Sin cewa, yana sa ran hukumomin kasar  za su bari shugabar hukumar kare hakkin bil'adama ta MDD Michelle Bachellet ta ziyarci kasar ba tare da wani kaidi ba, domin ziyartar wasu yankuna  ciki har da lardin Xinjiang na musulmi.

Guterres ya gana da shugaban kasar Sin Xi Jinping da ministan harkokin wajen kasar Wang Yi a gefen taron gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing a cewar rahoton na MDD.

Bachellet ta dade yana neman zuwa jihar Xinjiang domin gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi na  cin zarafin 'yan kabilar Uighur.

Hakan dai ya dagula dangantaka tsakanin Beijing da kasashen Yamma, inda Washington ta zargi Beijing da aikata kisan kiyashi, yayin da wasu kasashen da suka hada da Amurka suka kaurace wa wasannin Olympics na lokacin sanyi na kasar Sin.

Masu rajin kare hakkin bil adama sun ce cin zarafin da China ke yi wa 'yan kabilar Uighur ya hada da azabtarwa, tilastawa mutane aiki, da kuma tsare mutane miliyan daya a sansanoni.

China dai ta sha musanta zargin, tana mai cewa sansanonin cibiyoyin horaswa ne da aka kafa domin yaki da tsatsauran ra'ayi.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4034094

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: