Sakamkon bincike ya nuna cewa, ayyukan bankin musulunci na samun gagarumin ci gaba da bunkasa a kasar Uganda a cikin lokutan baya-bayan nan.
An yi marhabin da tsarin ba da tallafin Musulunci a Afirka a cikin 'yan shekarun nan a kasashe da dama saboda yawan musulmi.
Yawan matasa da karuwar fasahohin sadarwa tare da dimbin albarkatun arziki sun sa harkar hada-hadar kudi, tare da taimakon kudaden Musulunci ya fi yawa a nahiyar.
Haka lamarin yake hatta a wasu kasashen nahiyar da musulmi ke cikin tsiraru.
Baya ga zuba jarin da kasashen musulmi irinsu Qatar da Turkiyya ke yi a kasashen Afirka, har ila yau cibiyoyin ba da tallafin kudi ta Musulunci suna shiga tsarin hada-hadar kudi da bankunan kasashen.
A Afirka, kasashe irin su Afirka ta Kudu, Najeriya, Mauritius, Botswana, Kenya, Tanzaniya, Rwanda, Senegal, Aljeriya, Masar, Sudan da Tunusiya suna gudanar da harkar hada-hadar kudi ta Musulunci.
Bambance-bambancen imani na addini na al'ummomin kasashen da aka ambata, yana kara tabbatar da cewa bankin Musulunci yana samun gagarumin ci gaba.
Uganda na daya daga cikin kasashen da aka amince da tsarin ba da kudade na Musulunci da hada-hadar banki.
Kimanin kashi 11 cikin dari na al'ummar kasar miliyan 45 Musulmai ne. Tsarin samar da kudade na Musulunci a wannan kasa yana bunkasa kuma yana karuwa sakamakon kasancewar bakin haure daga kudancin Asiya da kuma musulmin kasar suna gudanar da harkokinsu a bisa wannan tsari.