IQNA

An fara gasar kur'ani ta duniya a Aljeriya tare da halartar kasashe 46

12:32 - February 19, 2022
Lambar Labari: 3486955
Tehran (IQNA) An fara gasar haddar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa ta Aljeriya karo na 17 tare da halartar kasashe 46.

Shafin Bawaba Al-Ahram ya bayar da rahoton cewa, A ranar alhamis ne aka fara gasar bayar da lambar yabo ta haddar kur'ani mai tsarki ta Aljeriya karo na 17 tare da halartar kasashe 46 daga ko'ina cikin kasashen musulmi.
Ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Aljeriya a cikin wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewa, a bana za a gudanar da gasar ne karkashin taken "da kuma karatun kur'ani" wanda kuma ya zo daidai da zagayowar ranar da manzon Allah (SAW) ya yi mi'irajinsa a watan Rajab, yayin da a wannan shekara ana gudanar da gasar ne sabanin shekarun baya, inda akan gudanar da gasar ne a watan Ramadan.
Sanarwar ta kara da cewa, saboda sharuddan da aka sanya na annobar Corona, za a gudanar da gasar ne ta hanyar fasahar sadarwar bidiyo, kuma za a gudanar da alkalancin ne karkashin wasu alkalai shida daga Masar daga Guinea da kuma alkalai hudu daga Aljeriya, kuma alkaliya mace guda daya.
Gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa ta Aljeriya, wacce aka fara gudanar da ita a shekarar 2004, ta kasance ta masu hadda 'yan kasa da shekaru 25, kuma za a bayar da kyautuka ga wdanda suka fi nuna kwazo, na daya zuwa na uku.
 
https://iqna.ir/fa/news/4037176

Abubuwan Da Ya Shafa: aljeriya
captcha