IQNA

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi a kasar Saudiyya

19:47 - March 15, 2022
Lambar Labari: 3487056
Tehran (IQNA) Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da kisan gillar da Saudiyya ta yi wa wasu fursunonin siyasa a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Youm cewa, a jiya litinin ne majalisar dinkin duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da hukuncin kisa da aka yi wa wasu ‘yan kasar Saudiyya 81 tare da yin Allah wadai da kisan gilla da aka yi a kasar Saudiyya.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya ta fitar da sanarwa a jiya Asabar cewa ta zartar da hukuncin kisa kan mutane 81, rabinsu 'yan Shi'a, bisa zarginsu da ta'addanci da karkatar da akida.

Hukuncin kisa da Saudiyya ta yi wa mutane 81 da suka hada da matasa 'yan Shi'a 41, ya janyo suka a yankin da ma duniya baki daya. Wasu fursunonin sun kasa da shekaru 15 a lokacin da aka kama su; A gefe guda kuma fursunonin Yemen da dama na daga cikin wadanda aka kashe, wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar Geneva kan fursunonin yaki.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4042998

captcha