IQNA

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 15 ga Maris a matsayin ranar yaki da kyamar Musulunci ta duniya

17:43 - March 16, 2022
Lambar Labari: 3487061
Tehran (IQNA) Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani kudiri da ta ayyana ranar 15 ga Maris a matsayin ranar yaki da kyamar Musulunci ta duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na yanar gizo na cewa, babban taron majalisar dinkin duniya a jiya Talata ya amince da wani kuduri mai taken "Ranar yaki da kyamar Musulunci ta duniya".

A cewar kudurin, yau 15 ga watan Maris aka ware ranar yaki da kyamar Musulunci ta duniya.

Kasashen musulmi ne suka gabatar da kudurin, kuma Iran da wasu kasashe biyar ne suka jagoranci shawarwarin kan wannan kudiri.

Kasashen musulmi da suka hada da Iran da Pakistan da Turkiyya da Saudiya da Jordan da kuma Indonesia ne suka jagoranci tattaunawar tare da jaddada aniyarsu ta yaki da kyamar Musulunci.

Kudirin ya yi Allah wadai da duk wani kalaman kyama da cin zarafi da ake yi wa musulmi tare da yin kira da a karfafa kokarin kasa da kasa na karfafa hakuri da juna da zaman lafiya.

Kudirin ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin kasa da kasa da su samar da ingantattun bayanai kan yaki da kyamar Musulunci da kuma gudanar da bukukuwan wannan rana.

 

https://iqna.ir/fa/news/4043306

captcha