IQNA

Sayyid Nasrallah: Babu Dakarun Hizbullah A Ukraine

17:17 - March 19, 2022
Lambar Labari: 3487071
Tehran (IQNA) Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hassan Nasrallah ya musanta kasancewar wani soja ko kwararre a cikin harkar a Ukraine.

A rahoton tashar Al-Manar, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya musanta kasancewar dakarun kungiyar a Ukraine a yammacin yau Juma'a.

Nasrallah ya shaidawa Al-Manar cewa: "Na musanta kasancewar mayakan Hezbollah ko kwararru a Ukraine da ke yaki tare da sojojin Rasha."

Ya kuma jaddada cewa: Babu wani daga cikin mayakan kungiyar Hizbullah, ko kwararre da ya je wannan fagen daga a Ukraine,.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ya ce kamata ya yi a nemi gwamnatin Lebanon ta kafa cibiyar kula da rikice-rikice; Domin sakamakon yakin ya kai kasar Labanon da kuma yankin.

A gefe guda kuma, Ali Dammush mataimakin shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah a baya-bayan nan ya zargi gwamnatin Amurka da alhakin farko da na karshe na abin da ke faruwa a Ukraine, domin a cewarsa, Amurka ce ta shirya da kuma matsa masa lamba kan hakan.

Ya kara da cewa, "Ukraine ta fada cikin tsarin siyasar Amurka na tashin hankali a duniya." Darasin da za mu koya shi ne, tallafin da Amurka ke ba wa ba gaskiya ba ne.

Maganar gaskiya ita ce, shugaban Ukraine da tsohon shugaban Afganistan, wadanda suka amince da Amurka, sun yarda cewa Amurka ta bar su su kadai.

A wani bangare na jawabin nasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa: Har yanzu ruhin wariya ne ke mamaye dabi'un masu da'awar wayewa da ci gaba da masu ikirarin  hakkin bil'adama.

A cikin kasashen da suka ci gaba da nuna cewa sun damu matuka da hakkin dan Adam, wato Amurka da Turai, muna ganin yadda ake mu'amala da bakaken fata.

Mataimakin shugaban kungiyar Hizbullah ya kara da cewa: Ruhin wariyar launin fata a kasashen yammacin duniya yana bayyana kansa a cikin abubuwan da suke faruwa a kasar Ukraine a wadannan kwanaki, kuma mun fahimci yadda kafafen yada labarai da 'yan siyasa na yammacin Turai suka bayyana wariyar launin fata, kuma suke mayar da Ukraine wata kasa mai wayewa sabanin sauran kasashe.

Ya ce ba mu yarda da yaki da kisan jama’a ba a ko’ina ne, amma mun ga yadda Amurka da kawayenta suka yi yake-yakea  duniya da kisan dubban darurwan fararen hula, duk wannan bai taba zama labari ba, kuma me yasa abin da yake faruwa a halin yanzu na kisan dubban faren hula da Saudiyya ke yi bai zama a labari a duniya ba, kamar yadda bai zama abin magana a wurin kasashen turai ba.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4044043

captcha