IQNA

Kungiyar Al-Shabaab ta kai hari hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya a Somaliya

20:01 - March 23, 2022
Lambar Labari: 3487084
Tehran (IQNA) Kafafen yada labarai sun rawaito cewa kungiyar ta'addanci ta Al-Shabaab ta kai hari a hedikwatar MDD dake kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na Mogadishu babban birnin Somaliya inda suka yi artabu da jami'an tsaro.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya habarta cewa, wasu majiyoyin labarai na cewa wasu daga cikin kungiyar ta'addanci ta al-Shabaab sun yi arangama da jami'an tsaro bayan da suka shiga wani gini kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na Mogadishu.

Tashar talabijin ta Somalia ta bayar da rahoton cewa, mayakan al-Shabaab sun kai hari a harabar Halan, hedkwatar rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, kuma an soke duk wani tashin jirage na cikin gida da na ketare a filin jirgin saman Mogadishu bayan harin.

Al-Arabiya ta bayar da rahoton cewa, al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin, inda ta ce ‘ya’yanta sun kutsa cikin wani katafaren gida da tawagogin kasashen Yamma ke jibge. Kungiyar ta ce ta kashe sojojin Somaliya da dama.

'Yan sandan Somaliya a cikin wata sanarwa da suka fitar sun ce, sun yi arangama da wasu gungun 'yan bindiga da ke shirin kai hari a sansanin sojojin Somaliya da ke kusa da filin jirgin saman Mogadishu.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na cewa, dimbin fasinjojin kasashen waje, da dama daga cikinsu ‘yan Afirka ne, sun yi ta harbe-harbe a kusa da filin jirgin. Wani ganau da ke wurin ya ce maharan sun bi ta kofar shiga sansanin ne suka fara harbe-harbe.

Al-Shabaab reshe ne na al-Qaeda da ke aiki a Somaliya da gabashin Afirka kuma ta aiwatar da ayyukan ta'addanci da garkuwa da mutane a cikin 'yan shekarun nan.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4044718

captcha