IQNA

Amir Abdullahian ya gana da Sayyid Hassan Nasrallah

15:16 - March 25, 2022
Lambar Labari: 3487090
Tehran (IQNA) A safiyar yau Juma'a a rana ta biyu ta ziyararsa a birnin Beirut, ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almanar cewa, A safiyar yau Juma'a a rana ta biyu ta ziyararsa a birnin Beirut, ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah.

A yayin ganawar, Hussein Amir Abdullahian da babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun tattauna batutuwan baya-bayan nan a yankin da kuma na kasar Lebanon.

Taron ya samu halartar jakadan Iran a Labanon da Mir Massoud Hosseinian babban darakta a ma'aikatar harkokin wajen kasar kan harkokin yankin Gabas ta tsakiya.

A safiyar yau ne Amir Abdullahian ya gudanar da taron hadin gwiwa tare da gungun masana harkokin siyasa da al'adu da shugabannin jam'iyyu da shugabannin cibiyoyin bincike da ministoci da wasu ‘yan majalisar dokoki na yanzu da na da, da kuma fitattun marubuta da 'yan jarida  na kasar Labanon.

A yayin da yake bayani kan muhimman manufofin harkokin waje na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Amir Abdullahian ya bayyana mahangar Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan ci gaban yankin, halin da ake ciki a kasashen Afganistan, Yemen, Palastinu, da kuma tsayin daka kan  matakan da suka dace da su.

An kuma tattauna batun Ukraine, tattaunawar Vienna da tsarin tattaunawar Iran da Saudiyya.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4044936

 

captcha