IQNA

Ba da gudummawar fenti don gyara masallaci mafi tsufa a Uganda

21:11 - March 26, 2022
Lambar Labari: 3487093
Tehran (IQNA) Babban kamfanin fenti a Uganda ya ba da gudummawar wasu kayayyakinta domin sake gyaran masallaci mafi dadewa a kasar.

Kamar yadda shafin jaridar The Tower Post ya ruwaito, shugaban kamfanin fenti na santosh Gumte Kansai Plascon ya kai fentin ga jami'ai a wurin ginin Masallacin Mbogo da ke Kampala da yammacin ranar Juma'a.

Shugaban kamfanin Santosh Gumte ya ce " sake ginin Masallacin Mbogo wani gagarumin lamari ne mai muhimmanci a Uganda." A matsayinmu na kamfani, mun ga ya dace mu hada kai da al’ummar musulmi wajen kiyaye kayayyakin tarihi na wannan masallaci mai dimbin tarihi, domin wurin ibada mai tarihi da ke cikin kasarsmu.

An gina wannan masallaci mai tarihi a shekara ta 1903. An sake gina wannan masallacin ne saboda yadda masallacin da ya gabata yake iya daukar mutane 400 kuma ba za a iya yin sallar Juma'a a cikinsa  ba. amma Masallacin da aka sake ginawa zai dauki mutane kusan 1,700.

Kansai Plascon ya sha ba da gudummawar fenti don taimakawa cibiyoyin addini a Uganda.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4045003

Abubuwan Da Ya Shafa: kamfanin fenti
captcha