IQNA

Dakarun Hashd Al-shaabi na Iraki Sun Kai Farmaki A Sansanonin 'Yan Ta'adda

22:45 - March 30, 2022
Lambar Labari: 3487106
Tehran (IQNA) Rundunar dakarun Hashad al-Shabi na kasar Iraki ta sanar da fara wani gagarumin aikin soji na yaki da ta'addanci a yankunan Anbar da Salah al-Din.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Ahd cewa, kwamandan ayyuka na lardin Ninawa, Salah al-Din da Al-Anbar tare da sassan da ke da alaka da su a Hashad al-Shaabi sun sanar da kaddamar da wani gagarumin aikin yaki da ta’addanci a cikin tsarin rundunar hadin gwiwa.

A cikin wannan samame tare da goyon bayan dakarun sojin sama na kasar Iraki ana gudanar da aikin share fage da kuma duba yadda za'a kawar da sansanonin 'yan ta'adda da kuma lalata wuraren buyarsu, domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankunan da 'yan ta'addan suke mamaye da su.

Bayan da aka nada sabon kwamandan kungiyar ISIL da kuma sauya dabarun kungiyar daga manyan ayyuka zuwa ayyukan kwantan bauana, an nuna damuwa game da karuwar ayyukan kungiyar ta'addanci da kuma sake dawo da iko da wasu sassan Iraki da Siriya.

A shekarar da ta gabata ne majalisar dokokin Iraki ta yi kira da a janye sojojin kasashen waje gaba daya musamman sojojin Amurka.

Ya zuwa yanzu dai Amurka ta ki janye sojojinta daga Iraki bisa wasu dalilai.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4045503

captcha