Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Ahd cewa, Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, zai gabatar da jawabi na addini a ranar Juma’a mai zuwa da karfe 8:30 na dare agogon Lebanon kan azumin watan Ramadan mai alfarma.
Za a watsa jawabin kai tsaye ta tashar Al-Manar.