Daruruwan musulmi ne suka hallara a dandalin Times da ke birnin New York a ranar Asabar din da ta gabata don gudanar da azumin watan Ramadan, inda suka gudanar da sallar tarawihi a karon farko a tarihin kasar Amurka, kamar yadda jaridar Al-Nahar ta ruwaito.
Kafofin yada labaran kasar Amurka sun bayyana cewa, a yammacin ranar Asabar din da ta gabata ne aka raba ma al’ummar musulmin abinci guda 1,500 domin ganin karshen wannan wata na Ramadan.
Daya daga cikin musulmin da suka halarci muzaharar ya ce: Musulmi ba sa azumi don kawai su fahimci halin da talakawa ke ciki; A’a, suna azumi ne domin su samu kusanci zuwa ga mahaliccinsu kuma Ubangijin Allah Madaukaki.
“Mun zo nan ne domin gabatar da addininmu ga wadanda ba su san Musulunci ba,” in ji shi a dalilin sallar tarawihi a tsakiyar birnin New York. Musulunci addinin zaman lafiya ne kuma addinin hadin kai da yaki da tashin hankali.
Yayin da yake ishara da rashin fahimta game da Musulunci a tsakanin da yawa daga wadanda ba musulmi ba, ya ce: "Muna kwadaitar da mutane zuwa ga salla, da azumi, da ayyukan kwarai, da kuma bayar da zakka."
Wannan Ba’amurke ya bayyana cewa: Alkur’ani wahayi ne na Ubangiji da aka saukar wa Annabinmu Muhammadu (SAW). Kamar abin da aka saukar wa Yesu da Musa. Dukkanmu mun hade. Dole ne mutane su daina yunkurin tarwatsa Musulmi da Kirista.