Wata sanarwar da ma’aikatar kula da aikin hajji da Umara ta Saudiyya ta fitar ta ce za’a kara adadin wadanda zasu zo aikin hajjin daga ketare zuwa miliyan daya.
Masu niyyar zuwa aikin hajjin na bana zasu kasance masu shekara kasa da 65, sannan ya kasance sun yi cikakkun alluran riga kafin cutar korona a cewar sanarwar da kamfanin dilancin labaren kasar na SPA ya rawaito.
Haka zalika maniyatan zasu nuna takardar gwajin dake nuna cewa basa dauke da cutar ta korona, sannan kuma za’a gudanar da aikin hajjin cikin kiyaye matakan yaki da cutar.
A bara dai ‘yan Saudiyya 60,000, mahukunatan kasar suka baiwa damar yin aikin hajjin, maimakon miliyan 2 da rabi da suka saba sauke farali kafin bullar annobar korona.