Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na makka cewa, a ranar 10 ga watan Afrilu ne aka gudanar da matakin farko na gasar kur’ani ta kasa da kasa ta kasar Saudiyya mai taken “Atr al-Kalam”, kuma a wannan rana an zabo mahalarta 4 daga cikin mutane 36 da suka cancanci shiga gasar. matakin farko za a kammala rubu'in karshe ne da mutane 24 da suka hada da mutane 12 a fagen karatu da kuma mutane 12 a fagen kiran sallah.
Seyed Jasem Mousawi, wani makaranci dan kasar Iran daga birnin Khuzestan na kasar Iran na daya daga cikin mutanen da suka kai daf da na kusa da karshe a daren jiya da kuri'ar alkalai.
An fara gudanar da wannan gasa mai taken Atr al-Kalam tun daga ranar farko ta watan Ramadan. Sama da mahalarta 40,000 daga kasashe 80 ne suka yi rijistar sunayensu don halartar gasar, wanda za a watsa a gidan talabijin na kasar Saudiyya a cikin wannan watan Ramadan. A zagayen farko na gasar, mahalarta gasar sun aika da sautin na su da aka nada zuwa ga gasar don yanke hukunci na farko.
Wadana suka kai matakin daf da na kusa da karshe sun fito ne daga kasashe daban-daban da suka hada da Birtaniya da Kanada da Saudiyya da Iraki da Masar da Aljeriya da Iran da Malaysia da Indonesia da kuma Turkiyya.