IQNA

Halartar Kiristoci a taron buda baki na musulmi a Yammacin Kogin Jordan

23:53 - April 11, 2022
Lambar Labari: 3487154
Tehran (IQNA) Kungiyar kiristoci a yammacin gabar kogin Bethlehem na hada kai da musulmi wajen shirya buda baki ga mabukata da kuma kawata titunan birnin albarkacin watan Ramadan.

Kamar yadda jaridar Arab News ta ruwaito.

Ayyukan agaji, da taimakawa wajen kawata tituna da kasuwanni, raba ruwa da dabino kafin buda baki, na daga cikin ayyukan da wadannan kiristoci suke yi a Bethlehem, Ramallah da Nablus a gabar yammacin kogin Jordan.

Khalil Kawa, Kirista mai shekara 41, yana ba masu wucewa ta hanyar dabino da ruwan sha a wani mararrabar hanya a Nablus, wani gari da Musulmi, Kirista da Samariyawa ke zaune tare. “A matsayina na Kirista, ba na jin cewa ina yin wani bakon aiki na raba dabino da ruwa ga masu azumi,” inji shi. Ba na son banbance tsakanin Musulmi, Kirista ko Samariyawa. Mu duka Falasdinawa ne.
Ya kara da cewa a shekarar 2013, ni da wasu gungun abokai mun kafa wata kungiyar matasa mai suna Nablus Tour. Mu rukuni ne na masu daukar hoto. Muna tafiya muna daukar hotuna a cikin birnin Nablus; A ranar maulidin Manzon Allah (SAW) muna raba kayan zaki da kuma yi wa garin ado a jajibirin watan Ramadan da ma lokacin bukukuwan Idi. Muna kuma raba dabino da ruwa ga masu azumi.

Ya kara da cewa: "Wannan wani kyakkyawan jin dadi ne da ba za a iya siffanta shi ba, musamman da yake mutane suna jiranmu suna tambaya kafin Ramadan ko mun shirya ko muna bukatar wani abu."

A birnin Ramallah, wata kungiyar matasa ta kaddamar da wani gangamin wayar da kan jama'a game da watan Ramadan mai taken "Yafiya da musabaha a cikin watan soyayya" da nufin isar da sako mai kyau a tsakanin al'ummomin addini.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4048352

 

captcha