IQNA

Sojojin yahudawan Isra'ila Sun Kaddamar Da Wani Farmaki A Yau A Kan Masallacin Quds

17:07 - April 21, 2022
Lambar Labari: 3487200
Tehran (IQNA) a ci gaba da keta alfarmar masallacin Quds da yahudawa ke yi, a yau ma sun sake kaddamar da wani farmakin a kan wannan masallaci.

Da saifyar yau Alhamis ne dai sjojin Isra'ila su ka fara shiga cikin haraba da farfajiyar masallacin, inda su ka rika harba hayaki mai sa hawaye da abubuwa masu kara akan masu yin I’itikafi a bangarorin mata da mata dake ciki,tare da tilasta musu fitowa.

Bugu da kari, sojojin Isra'ila sun kuma yi amfani da kulake da hannu wajen dukan palasdinawan da suke cikin masallacin,kamar yadda kafafen watsa labaru su ka rika nuna abinda yake faruwa kai tsaye.

Bayan wani lokaci kadan, yahudawa ‘yan share wuri zauna da su ka kai dari bakwai da sattin da biyu sun kutsa cikin harabar masallacin ta kusurwowi daban-daban inda su ka rika gudanar da ibadarsu ta yahudanci a cikinsa.

Yau kwanakin biyar kenan a jere da yahudawan suke kutsawa cikin masallacin na Kudus mai albarka.

4051415

 

 

captcha