IQNA

Kimanin Mutane Dubu 250 Suka Raya Lailatul Qadr A Daren Jiya A Masallacin Quds

14:50 - April 28, 2022
Lambar Labari: 3487226
Tehran (IQNA) A yau Alhamis sojojin mamaya na Isra'ila sun harba barkonon tsohuwa kan masu ibada a harabar masallacin Al-Aqsa.

A cewar majiyoyin yankin, sojojin mamaya sun harba barkonon tsohuwa kan masu ibada a cikin masallacin Al-Aqsa, bayan kammala ayyukan ibada na Laylatul Kadr.

Majiyoyin Falastinawa sun tabbatar da cewa kimanin masu ibada kusan kwata milyan ne suka gudanar da ibadar daren lailatul kadari daren ashirin da bakwai ga watan Ramadan a cikin masallacin Al-Aqsa mai albarka.

Ma'aikatar da ke kula da harkokin addinin muslunci a birnin Kudus ta bayyana cewa: Masallata dubu 250 ne suka yi tururuwa zuwa masallacin Al-Aqsa domin raya  daren lailatul kadari, a cikin tsauraran matakan da mahukuntan mamaya suka dauka kan birnin.

Falastinawa da dama da suka halarci wurin da ma wadanda ba su halarta ba sun nuna farin cikinsu matuka, musamamn ma ganin cewa wannan lokaci da dadadi mai yawa na al’ummar musulmi suka halarci wannan wuri domin ayyukan ibada, duk da irin matakan takurawa da Isra’ila ta dauka, wanda yake kara tababtar da cewa har yanzu masallacin Quds yana a matsayin wuri mafi tsarki ga al’ummar musulmi na Falastinu a cikin kasarsu da yahudawa suka mamaye.

4053210

 

 

captcha