IQNA

Sayyid Nasrallah: Arcewar Sojojin Isra'ila Daga Kudancin Lebanon Sakamako Ne Gwagwarmayar Al'ummar Kasar

13:50 - May 26, 2022
Lambar Labari: 3487344
Tehran (IQNA) A jiya Laraba ne babban sakataren kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah ya bayyana cewa: gwagwarmayar al’ummar Lebanon ta kara karfi fiye da kowane lokaci a tarihi.

A cikin jawabinsa na tunawa da cikar shekaru 22 da 'yanto yankunan Lebanon daga mamayar Isra’ila, Sayyid Nasrallah ya tabbatar da cewa "ranar nasara a kan Isra'ila da 'yanto yankunan Lebanon” na daya daga cikin ranakun tarihi a kaar da ma yankin baki daya."

Ya ci gaba da cewa, suna godiya ga Allah wanda shi ne ya taimaka musu wajen samun wannan nasara, kuma ya ba su damar yin wannan zabi na mikewa da kansu domin kwatar ‘yancinsu da kare kasarsu da kansu, ba tare da sun jira taimakon kasashen larabawa ba.

Sayyid Nasrallah ya gode wa wadanda suka samu raunuka bisa ga abin da suka bayar na gudunmawa, da fursunonin da suka yi hakuri tsawon shekaru a gidan yari na yahudawa ‘yan mamaya, da kuma iyalai masu hakuri da juriya a kauyukansu da kuma a dukkan sassa na Lebanon.

Baya ga haka kuma ya jinjina bangarorin da suka kasance tare da al’ummar kasar Lebanon wajen fuskantar Isra’ila, da hakan ya hada da al’ummomin musulmi da na larabawa da kuma masu ‘yancin tunani da lamiri a duniya, da kuma kafofin yada labarai masu kokarin bayar da rahotanni na gaskiya, ba tare da tasirantuwa da farfagandar kafofin yada labaran yahudawa da na kasashen yammacin turai da ‘yan korensu ba.

 

4059732

 

 

captcha