IQNA

16:15 - May 27, 2022
Lambar Labari: 3487349
Tehran (IQNA) Malamar falsafa, marubucita kuma mai fassarar kur'ani 'yan kasar Italiya ta lashe lambar yabo ta kasa da kasa ta tattaunawa tsakanin addinai a shekarar 2022 a Qatar.

Taron tattaunawa tsakanin addinai karo na 14 na Doha, mai taken "Maganganun Kiyayya a Addinai; A aikace kuma a cikin matani" a Doha, wanda ya fara ranar Talata, 3 ga Yuni, ya kawo karshe tare da girmama wadanda aka zabi ayyukansu.

Sabrina Lei, a halin yanzu shugabar Cibiyar Buga littafai da Bincike ta Tawassul, tana ɗaya daga cikin waɗanda aka girmama a taron.

Cibiyar Tawassul ta mayar da hankali ne wajen gina wata gada tsakanin kasashen musulmi da kasashen yammacin duniya ta hanyar shirya tattaunawa ta addini da kuma yada sakon Musulunci cikin lumana, inda ta bayyana irin ayyukan da cibiyar ke yi, wadanda suke alfahari da samar da su.

Wannan fitacciyar malama ta fassara litattafai na addinin musulunci sama da 50 zuwa Italiyanci, da kuma littafai na Musulunci a cikin harshen Italiyanci.

Ta fassara Alkur'ani daga harshen Turancin Ingilishi na Abdullahi Yusuf Ali zuwa Italiyanci.

Taron tattaunawa tsakanin addinai na Doha, an fara gudanar da shi a shekara ta 2003.

Babban abin da aka fi mayar da hankali a taron na kwanaki biyu shi ne "Ma'anar kalaman kiyayya da dalilansa", "nau'oin kalaman kiyayya" da "Hanyoyin magance kalaman kyama".

4059817

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Qatar ، Malamar falsafa,
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: