Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, mahimmin ayyukan Imam Khumaini (r.a) kan yanayi da tsarin al’ummar duniya shi ne babban abin da zaman zai yi dubi a kansa.
Hojjatoleslam Abu Turabi Fard, Limamin Juma'a na Tehran na wucin gadi, Michel Kaadi, malamin addinin kirista na kasar Labanon, Hojjatoleslam Sheikh Abdullah Daqaq, malamin gwagwarmayar Bahrain kuma daraktan makarantun hauza a birnin Qum, da Sheikh Ghazi Yousef Hanineh shugaban mabiya mazhabar Shafi'i., suna daga cikin masu bayani a taron.
Tarurukan za su gudana ta hanyar Bidiyo, kuma za su mayar da hankali ne kan batutuwa da Imam Khumaini (RA) ya yi tsokaci kansu da kuma tsarin kasa da kasa, da ra'ayin juyin juya hali da kwayar mulkin zalunci a duniyar Musulunci a mahangar Imam Khumaini (RA) da kuma yunkurin Musulunci.
A ranar Laraba 1 ga watan Yuni da misalin karfe 10:00 na safe ne za a fara gudanar da taron kai tsaye a yanar gizo.
Abin tuni shi ne cewa wannan taron zai kasance ne ta hanayar yanar gizo, kuma ga masu sha'awar shiga, za a tura adireshi gare su.
https://iqna.ir/en/news/3479121