IQNA

Mahmoud Shahat a wajen bukin haddar Alqur'ani

17:23 - June 13, 2022
Lambar Labari: 3487413
Tehran (IQNA) An gudanar da bikin karrama fitattun mahardatan kur'ani mai tsarki a gaban matashin nan kuma shahararren makaranci na kasar Masar "Mahmoud Shahat Mohammad Anwar a lardin "Sharqiya" na kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Shorouk cewa, Osama Al-Azhari mai baiwa shugaban kasar Masar shawara kan harkokin addini shi ma ya halarci bikin da aka gudanar a cibiyar al-Husaini da ke yankin Gabashin kasar.

Sheikh Osama Al-Azhari da Shaht Anwar sun yaba da matakin da mahalarta gasar suka taka da iya karatunsu da haddar su, tare da taya mafificin alheri.

Al-Azhar malamin kur’ani a birnin Azhar, ya jagoranci gasar haddar kur’ani ta Manjo Janar Adel Hassanin, kuma a cikin wannan shiri an karrama fitattun malaman haddar da kuma daukar hoto na tunawa.

https://iqna.ir/fa/news/4063936

 

captcha