IQNA

Isma'il Haniya Ya Jaddada Goyon Bayan Hamas Ga Gwamnatin Kasar Lebanon

16:38 - June 27, 2022
Lambar Labari: 3487475
Tehran (IQNA) Shugaban ofishin siyasa na Hamas Ismail Haniyeh ya ce  tawagar Hamas ta gana da Firayi ministan Lebanon Najib Mikati, a yau Litinin a birnin Beirut.

Haniyah ya kara da cewa: “Mun kuma nuna masa matukar jin dadinmu da gudanar da ziyarar da tawagar shugabannin kungiyar suka kai kasar Lebanon, sannan mun kuma taya shi murnar sake nada shi shugabancin gwamnati, muna kuma yi masa fatan samun nasarar kafa wannan gwamnati yadda ya kamata, ta yadda za ta iya magance matsalolin da ake da su a Lebanon."

Ya kara da cewa, "Mun gabatar da bayanin kan halin da ake ciki a Falastinu musamman a birnin Kudus da masallacin Al-Aqsa mai albarka, da ke gabar yammacin kogin Jordan, kamar yadda kuma mun bayyana masa halin da ake ciki a yankin zirin gaza da Isra’ila ke ci gaba dea killace shi.

Haniyah ya ci gaba da cewa, mun tabbatar da hadin kanmu da 'yan'uwa a kasar Lebanon dangane da duk wani aiki na wuce gona da iri na Isra’ila  kan albarkatunta da iyakokinta.

Haniyah ya yaba da matsayar da ya ce Lebanon ta dauka kan batun shata iyaka da Palastinu da Isra’ila ta mamaye da kuma batun albarkatunta, yana mai nuni da cewa tatatunawarsu da Mikati da sauran bangarorin Lebanon ta yi armashi matuka.

 

4067040

 

captcha