Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Mamdouh Amer, Mahmoud Shahat Anwar, da Abdul Basit Muhammad Abdel Samad, mashahuran makarantun kasar Masar, da kuma “Eidi Shaaban”, wani mashahurin mai karatu na zamani dan kasar Tanzania, sun karanta suratul Dhuha a cikin wannan fim.
Baya ga Abdul Basit, mawallafa ukun da aka ambata a cikin wannan fim sun karanta Suratul Dhuha cikin numfashi guda, wanda ya samu karbuwa da jinjina daga wadanda suka halarci bikin.