IQNA

Kare muhalli ta hanyar dasa itatuwa dubu a cibiyar Musulunci ta Canada

16:38 - August 04, 2022
Lambar Labari: 3487638
Tehran (IQNA) Musulman wata cibiya ta addinin musulunci a birnin Alberta na kasar Canada, sun aiwatar da wani shiri na dasa itatuwa dubu a kewayen cibiyar domin taimakawa wajen farfado da muhallinsu tare da taimakon koyarwar addinin musulunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Fort McMurray Today cewa, mambobin masallacin Fort McMurray da cibiyar musulunci ta jihar Alberta, domin kare muhallinsu, sun dasa itatuwa 100 a matsayin kashi na farko na shirin dasa itatuwa dubu a kewayen wannan wurin ibada na musulmi.

Muhammad Al-Zubaidi shugaban cibiyar Musulunci ya ce: Annabinmu ya ce ko a karshen rayuwa idan ka ga ranar kiyama ta kusa, kuma kana da bishiya ko karamar tsiro a hannunka, to ka dasa ta. .

Ya kara da cewa: Wannan yana nuna cewa yana da matukar muhimmanci a mahangar Musulunci a dasa itatuwa gwargwadon iyawarka.

Al-Zubaidi ya ci gaba da cewa samun itatuwa da ciyayi a yankin masallacin wani bangare ne na al'adun Musulunci da ke wartsakar da al'umma da kuma amfani ga muhalli.

Ya kara da cewa: Na san cewa sauye-sauye da dama suna faruwa a wannan yanki kuma mutane da yawa suna ƙaura zuwa yankuna daban-daban saboda ayyukansu. Na gode don samun damar ci gaba da wannan aikin.

Wannan masallacin da ke samun halartar masallata kusan 2000 a duk mako, yana da dakin sallah da dakin wasanni. Kashi na biyu na masallacin kuma ya hada da ginin kasa da bene na biyu da ake ginawa.

4075922

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: karshen rayuwa ، Kare muhalli ، cibiya ، addinin muslunci ، dasa itatuwa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha