IQNA

Nasrallah: Ayyukan Ta'addancin Isra'ila Ba Za su Wuce Ba Tare Da Martani Ba

20:15 - August 07, 2022
Lambar Labari: 3487652
Tehran (IQNA) babban sakataren kungiyar Hizbullah ya jaddada cewa ayyukan ta'addancin Isra'ila ba zu wuce ba tare da martani ba.

Babban sakatare Janar din kungiyar ta Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah da yake jawabi kan ranar Tasu’a wato 9 ga watan Muharram a yankin Dahiya dake binrin Berut ya mika Taa’ziyya ga kungiyar Jihdil islami kan shahadar kusa a kungiyar Tayseer Jabari sakamakon harin ta’addanci da Isra’ila ta kai a yankin Gaza,

Nasarullah ya bayyana kisan gillan da Isra’ila ta yi wa dan gwagwarmayar a matsayin Taddanci da ya kamata kowa yayi tir das hi,yace mayar da martani da dakarun gwagwarmaya suka yi kan Isra’ila yayi daidai ,

Haka zalika ya gargadi Isra’ila game da duk wani kuren lisssafi kan kasar Lebanon domin hizbullah sun kara karfi fiye da kowanne lokaci a baya kuma ba za ta taba daga kafa ko kadan kan hakkin kasarta ba.’

Da yake mayar da martani game da barazanar da ministan kudi na Isra'ila yayi na shafe yankin Dahiya yace kwanaki da za su zo nan gaba ne kawai za su bayar da Amsa kan wannan barazanar, domin kuwa dakarun gwagwarmar falasdinu da na labanon sun tabbatar cewa za’a iya yin galaba kan dakarun Isra’al kuma a wulakanta su.

Haramtacciyar kasar Isra'ila dai ta fara kaddamar da hare-haren baya-bayan nan ne a kan al'ummar zirin Gaza tun daga ranar Juma'a da ta gabata, inda ya zuwa yanzu cikin kwanaki biyu ta kashe mutane talatin da hudu, da suka hada da mata da kananan yara takwas.

 

4076496

 

 

 

 

captcha