IQNA

Iyalan Yaran Da Isra'ila Ta Kashe A Gaza Sun Bukaci Kotun Duniya Ta Hukunta Gwamnatin Yahudawan

9:09 - August 18, 2022
Lambar Labari: 3487706
Tehran (IQNA) Bayan bayyana laifukan da gwamnatin yahudawan Isra’ila ta tafka  na kisan kananan yara a yankin Jabalia da ke arewacin zirin Gaza a baya-bayan nan, iyalan wadanda lamarin ya shafa  sun bukaci a hukunta Isra’ila a gaban kotun kasa da kasa.

Shafin yada labarai na tashar  Aljazeera ya bayar da rahoton cewa, bayan da sakamakon binciken ya tabbatar da cewa gwamnatin Isra’ila c eta aiwatar da kisan gillar da aka yi wa kananan yara 5 a yankin Jabalia da ke arewacin zirin Gaza, iyalan wadannan yara sun bukaci a gurfanar da mahukuntan Isra’ila a gaban kotu.

Wadannan yara sun yi shahada ne a  harin baya-bayan nan da yahudawan sahyuniya suka kai a zirin Gaza.

Jaridar Haaretz ta bayyana a cikin wani rahoto cewa: A wancan lokaci sojojin Isra'ila sun yi ikirarin cewa an kashe wadannan yara ne sakamakon fadowar makamin roka na Saraya al-Quds (reshen soja na kungiyar Jihad Islami) a yankin Jabalia.

Iyalan yaran biyar kuma sun jaddada wajibcin gurfanar da firayi ministan Isra’ila kan wannan laifi a gaban kotun duniya, kasantuwar shi  ne keda hannu kai tsaye wajen kai hare-haren.

A yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a wurin janazar  kananan yaran a sansanin Jabalia, iyalai da suka rasa rayukansu sun bukaci hukumar Palasdinawa da ta dauki nauyin shigar da wanan kara kan kisan kananan yara da Isra’ila ta yi.

 Haka nan kuma iyalan wadannan yara sun yi Allawadai da yadda gwamnatocin kasashen larabawa suka yi gum da bakunansu kan wannan mummunar ta’asa da Isra’ila ta aikata, da kuma yadda wasunsu ma suke ta hankoron ganin sun kulla hulda da Isra’ila a cikin irin wannan yanayi.

 

4078709

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha