IQNA

Hamas ta yi Allah-wadai da sabon shirin Isra’ila na tsugunar da yahudawa a birnin Kudus

19:25 - August 18, 2022
Lambar Labari: 3487710
Tehran (IQNA) Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a yayin da take yin Allah wadai da sabon shirin Isra’ila na gina matsugunan yahudawa a birnin Quds, ta bayyana wannan mataki a matsayin wani sabon mataki na mayar da yankunan Palastinawa na yahudawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar yada labaran Falasdinu ta bayar da rahoton cewa, kungiyar Hamas ta yi kakkausar suka ga shirin gina matsugunan da gwamnatin sahyoniyawan ta ke yi a yankunan Palastinawa da ta mamaye musamman birnin Quds.

Wannan bayani yana cewa: Makiya yahudawan sahyoniya suna ci gaba da aiwatar da wadannan tsare-tsare na gina matsugunan wanda hakan  wani yunkuri ne na goge burbushi da alamomin tarihin musulunci a birnin Quds.

Hamas ta jaddada cewa: Al'ummar Palastinu za su yi yaki da wannan manufa ta makiya, tare da hadin kai da gwagwarmaya tare domin kare hakkokinsu.

Wannan yunkuri ya bayyana cewa: Al'ummar Palastinu sun nuna sadaukarwa da dama a wannan fage ta hanyar tsayin daka a duk fadin yankunan  yammacin kogin Jordan musamman birnin Quds.

A jiya ne dai gwamnatin yahudawan sahyoniya ta sanar da amincewa da shirin gina sabbin gidaje 434 a yankin Sur Bahr da ke gabashin birnin Kudus da ta mamaye, domin tsugunnar da yahudawa da suke yin hijira daga kasashen duniya, zuwa Falastinu da Isra’ila ta mamaye.

4078963

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: burbushi ، birnin Quds ، musamman ، cibiyar ، tarihi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha