IQNA

Majalisar Dinkin Duniya: Ya kamata Taliban ta yi kokarin dakile hare-haren ta'addanci

19:06 - August 19, 2022
Lambar Labari: 3487712
Tehran (IQNA) A yayin da take ishara da karuwar hare-haren ta'addanci a Afganistan, tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta bayyana nadama kan ci gaba da kai wadannan hare-hare tare da neman karin matakan da suka dace daga kungiyar ta Taliban domin dakile wadannan hare-haren ta'addanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ofishin kula da ayyukan agaji na majalisar dinkin duniya a kasar Afganistan (UNAMA) ya fitar da sanarwa tare da sanar da cewa: mutane 250 ne suka mutu ko kuma suka jikkata sakamakon hare-haren bama-bamai da aka kai a cikin ‘yan makonnin nan kadai a wannan kasa.

Har ila yau, wannan ofishin ya bayyana nadamar harin da aka kai kan masu ibada a cikin wani masallaci a birnin Kabul a jiya, ta hanyar wallafa jerin sakonnin Twitter a shafinsa na hukuma.

Fashewar ta faru ne da yammacin jiya a masallacin "Sadiqiyeh" da ke yankin Khairkhane na birnin Kabul. A cewar Hotunan da aka wallafa na wannan fashewar, adadin masu ibada na wannan masallaci sun mutu ko kuma suka jikkata sakamakon fashewar.

Ko da yake jami'an tsaron Taliban ba su ce komai ba game da adadin wadanda suka mutu a wannan fashewar, tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, ta nakalto daga majiyar tsaro cewa mutane 20 ne suka mutu yayin da wasu 40 suka jikkata a wannan fashewar. UNAMA ta kuma ce mutane da dama ne suka mutu ko kuma suka jikkata a wannan fashewar.

A cikin kwanaki goma na karshen watan Muharram, a yammacin birnin Kabul shi ma an samu wasu munanan fashe-fashe guda biyu. A cewar Majalisar Dinkin Duniya, mutane 120 ne suka mutu ko kuma suka jikkata a wadannan fashe-fashe guda biyu. Duk da alkawuran da 'yan Taliban suka dauka na tabbatar da tsaron tarukan makokin Muharram, Taliban ba za ta iya hana wadannan hare-hare ba.

 

4079045

 

 

captcha