IQNA

Wani fitaccen siyasa a kasar  Sweden ya nuna adawa da matakin kona kur’ani da Paludan ke yi a kasar

19:19 - August 19, 2022
Lambar Labari: 3487713
Tehran (IQNA) Dan siyasar kasar Sweden Jan Eliasson, yayin da yake nuna adawa da kona kur’ani a kasarsa, ya bayyana kashe kudi domin tallafawa Rasmus Paludan a matsayin mara amfani.

A bayanin da cibiyar yada labarai ta Al-Markaz Al-Sweidi ta bayar, Jan Eliasson, shugaban jam'iyyar Socialist Party mai mulki a kasar Sweden, a cikin bayanansa na ‘yan siyasa masu kyakykyawan ra'ayi  a kasar, ya ce yana son aiwatar da wata doka a kasar Sweden da ta ba da damar hukunta wadanda suka aikata laifin kona Alqur'ani da littafai masu tsarki.

Ya kara da cewa: "Bayar da miliyoyin daloli don kare zanga-zangar masu tsattsauran ra'ayi hauka ne, kuma wannan ba kare fadar albarkacin baki ba ne, kamar yadda kuma yana zubar da kimar Sweden matukar za ta bayar da kariya ga masu zagin addinin wasu da kuma kona littafansu da suke da tsarki a cikin akidarsu.

Wannan dan siyasar na Sweden ya bayyana cewa rashin hankali ne a kashe miliyoyin kudi  don kare laifin kona kur'ani da wani mai tsatsauran ra'ayi ya yi, ya kuma bukaci a kafa dokar da za ta dakatar da wannan mataki maras amfani.

A cewar shugaban jam'iyyar Socialist Party mai mulkin kasar Sweden, a cikin babi na 16, sakin layi na 8 na dokokin hukunta manyan laifuka na wannan kasa, tunzura jama'a ko wata kabila a cikin al'umma ta hanyar magana ko aiki babban laifi ne, kuma ya cancanci hukunci na haifar da yanayi na rashin doka da oda a kasa.

4079137

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hauka ، zubar da kima ، nuna adawa ، mara amfani ، tsaki
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha