IQNA

Shirye-shirye Arbaeen na shekara ta 2022 a iyakar Iran da Iraki

KHORRAMSHAHR (IQNA) yankin  Shalamcheh a lardin Khuzestan na shirin karbar bakuncin miliyoyin maziyarta da za su gudanar da tattakin Arbaeen a makwabciyar kasar Iraki.

A matsayin daya daga cikin manya-manyan tarukan addini a duniya, Arbaeen shi ne cika kwanaki 40 bayan Ashura, ranar shahadar jikan Manzon Allah SAW, Imam Husaini (AS). Ranar Arbaeen ta zo ne a ranar 17 ga watan Satumban wannan shekara.

Abubuwan Da Ya Shafa: Shirye-shirye ، arbaeen ، karbar bakunci ، miliyoyin maziyarta