IQNA

Kafa baje kolin kur'ani karo na uku akan hanyar tafiya ta Arbaeen

14:23 - September 10, 2022
Lambar Labari: 3487830
Tehran (IQNA) Cibiyar kula da kur'ani ta Najaf Ashraf dake da alaka da Majalisar Darul Kur'ani ta Haramin Abbas (AS) ta sanar da gudanar da baje kolin kur'ani karo na uku a kan hanyar Najaf Ashraf zuwa Karbala.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban wannan cibiya Mohanand Al-Miyali ne ya sanar da hakan yana mai cewa: Wannan baje kolin ya hada da rumfuna guda bakwai don gabatar da kur’ani, bincike, yada labarai da sauran ayyukan wannan cibiyar, wadanda ake gudanar da su a cikin layi daya, tare da yada ilimin Alqur'ani. A cewarsa, wannan baje kolin kur’ani zai dauki tsawon kwanaki 10.

Al-Miyali ya kara da cewa: A gefen wannan baje kolin, za a kuma gudanar da gasar da'irar kur'ani mai girma da gasar kimiyya da ilimi.

A daya hannun kuma an kafa bangaren tajwidi  a karkashin kulawar malamai da masu kula da cibiyar, sannan za a raba kasidu na ilmantarwa da farfaganda a tsakanin maziyarta.

A cikin wannan baje kolin kuma wani mai bincike daga sashin bincike da wani malami daga sashin kula da harkokin kur’ani ma sun hallara domin amsa tambayoyi na bincike da na addini da na shari’a da na kur’ani na maziyartan.

Shi ma daraktan cibiyar kula da kur’ani ta Najaf Ashraf ya sanar da gudanar da gasar kur’ani mai tsarki tare da tambayoyi mabanbanta talatin da nufin karfafa gwiwar maziyartan amfanuwa da baje kolin.

 

4084347

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: baje koli ، amfanuwa ، karfafa gwiwa ، maziyarta ، tafiya ta Arbaeen
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha