IQNA

Makarantar tauhidi ta Khan a Yazd

YAZD (IQNA) – makarantar tauhidi ta Khan daya ce daga cikin makarantun hauza na tarihi a lardin tsakiyar kasar Iran wadda aka kafa  a shekara ta 1772.

Muhammad Taghi Khan daya daga cikin mashahuran sarakunan Yazd ne ya bada umarnin gina makarantar. Makarantar tana cikin yanayin tarihi na birnin Yazd, makarantar tana da fadin murabba'in mita 2,910 kuma tana da fili uku.

'Yan yawon bude ido na Iran da na kasashen waje suna ziyartar wurin a lokacin hutun makaranta don ganin irin gine-ginen da ya yi na daukar ido wanda ya koma zamanin Zandiyeh da Qajar.