IQNA

‘Yan kallon gasar cin kofin duniya ta Qatar na maraba da kiran sallah

18:01 - December 02, 2022
Lambar Labari: 3488270
Tehran (IQNA) Baki da suka halarci gasar cin kofin duniya a kasar Qatar sun yi maraba da kiran salla a masallacin "Katara" da ke kasar Qatar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Tawaswal cewa, hoton bidiyon kiran salla a wannan masallaci da aka fitar ya nuna lokacin da wasu da ba ‘yan Qatar ba suka shiga masallacin. Yayin da suke nadar kiran sallah da wani shehi yayi da wayoyinsu.

A cikin wannan faifan bidiyo, an ga yadda masu sha'awar gasar cin kofin duniya ke nuna mamaki da sha'awarsu; Kamar dai suna fuskantar lokatai na ruhaniya.

Bidiyon wannan lamari ya dauki hankula sosai a shafukan sada zumunta inda wasu suka bayyana cewa wadannan wadanda ba musulmi ba za su so wani ya jagorance su kan tafarkin addini da kuma bayyana musu koyarwar Musulunci da koyarwarsa ta lumana.

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kiran sallah ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha