An watsa wani karatun da Muhammad Awad Al-Imami daya daga cikin makarantun duniyar musulmi ya yi na ayoyin da suka shafi labarin Maryama (AS) da kuma haihuwar Annabi Isa Almasihu (A.S) a cikin Alkur’ani mai girma.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Muhammad Awad Al-Amami daya daga cikin makarantun duniyar musulmi ya karanta aya ta 16 zuwa ta 30 a cikin suratul Maryam da kuma sauti mai taken “Labarin Haihuwar Almasihu (AS)”